ME KE SA MOTSIN MARA KO MAHAIFA GA MACEN DA BATA DA CIKI KUMA WANE IRIN MATAKI YA KAMATA A ƊAUKA?--------------------
ME KE SA MOTSIN MARA KO MAHAIFA GA MACEN DA BATA DA CIKI KUMA WANE IRIN MATAKI YA KAMATA A ƊAUKA?
Mata dayawa suna jin mahaifar su ko marar su na motsi duk da ba juna-biyu ke ga re su ba. Wasu suna jin motsin kamar kicking na jariri a cikin ciki.
Abubuwan da ke iya sa mace ta ji haka su ne kamar haka;
1. Tsokar mahaifa na irin wannan motsi idan aka samu canjin sinadaran hormones a jikin mace.
2. Ovarian cyst na iya saka mace ta ji mahaifar ta na motsi haka kawai
3. Damuwa da kuma bakin ciki na saka haka
4. Motsin hanjin ciki na saka haka
5. Infection din mahaifa
MATAKIN DA YA KAMATA A ƊAUKA
---------------------
Sau da dama irin wannan motsin ba ya da matsala kuma ba sai an ɗauki mataki ba. Yana zama matsala ne idan jini na zuba ko kuma idan yana saka wa mace ciwo sosai ana yin test kuma a sha magani sai a dace da ikon Allah.
Allah Shi ƙara mana lafiya.
Asibiti a Tafin Hannun ka
Asibiti A Tafin Hannun Ka
#fahimtarlafiya #arewahealth #asibitiatafinhannunka #arewawomen #AREWA24 #asibiti #kano #arewa #Nijar #LAFIYA
Comments
Post a Comment